<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>152</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Zo wurin Yesu, kada ku ƙi,
 Yesu ke nemanmu duka mu bi.
 Kada ku tsaya, yau sai ku ji,
 Yesu ke kiranku.

[V2]
 KORUS
 Murna, murna, murna za mu yi,
 Masu zuwa, Yesu ba ya ƙi.
 Can za mu taru tare da shi,
 Can cikin mulkinsa.

[V3]
 2) Yara, in ji shi, su na ke so,
 Duk ƙanƙanana ku bar su su zo,
 Kada ku hana wanda ya so,
 Amma ku karƃe su.
 Korus

[V4]
 3)Yesu ne hanya, Yesu ne rai,
 Makiyayi mai aminci ne dai.
 Shi za ya bi da nasa sosai
 Har zuwa gidansa.
 Korus</lyrics>
<title>Zo Wurin Yesu, Kada Ku Ƙi LW152</title>
</song>